Alheri gadon barci: Wani da rikicin Kaduna ha rutsa da shi ya kai ma El-Rufai ziyarar godiya
Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya karbi bakoncin wani matashi da rikicin jahar Kaduna na baya bayan nan ta rutsa da shi, har ma ya jikkata, Geoffrey Mathias, a fadar gwamnatin jahar Kaduna dake gidan Sir Kashim Ibrahim.
Legit.com ta ruwaito Mathias mai shekaru 24 ya kai ma gwamnan ziyarar ne domin ya gode masa bisa kulawar da ya nuna masa yayin da yake jinyar raunin daya samu a Asibiti, inda El-Rufai ya kaikkai masa ziyara don duba halin da yake ciki.
KU KARANTA: Bango ya tsage: Bahallatsar tsige Oshimole ya raba kawunan jiga jigan yayan jam’iyyar APC

Asali: Twitter
Mathias ya kai ma Gwmana El-Rufai ziyarar godiyar ne a ranar Talata 6 ga watan Nuwamba tare da iyayensa da yan uwansa.
Idan za’a tuna rikicin Kaduna ya soma ne daga kasuwar magani a wata ranar Alhamis, ranar da kasuwar ke ci, sakamakon hatsaniya tsakanin yan asalin garin da baki masu zuwa cin kasuwa, wanda yayi sanadiyyar asarar rayuka da dama.
Wannan rikici na kasuwar magani ne ya haifar da wata sabuwar rikici a cikin garin Kaduna a ranar Lahadin da ta biyo, wanda shima ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a cikin garin.

Asali: Twitter
Kamar abin ya kare, sai kwatsam wani sabon rikicin ya barke a ranar Juma’ar da ta biyo a cikin garin Kaduna, dalili kuwa shine barayi masu garkuwa da mutane sun halaka sarkin kabilar Adara, Nuhu Galadima bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki.
Kisan wannan basarake ne ya tunzura yayan kabilarsa suka fara tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka farfasa ma matafiya motoci, amma basu kai ga fara kashewa ba jami’an tsaro suka tarwatsa su, tare da kama wasu daga cikinsu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng