Har gobe Hajiya Zainab Shamsuna ce Ministar kudi a Gwamnatin Najeriya
- An fara rade-radin cewa Shugaban kasa Buhari ya canza Ministar kudi a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta dai karyata wannan jita-jita da ke ta faman yawo a ko ina
- Wasu rahotanni na yawo cewa an maida Udo Udoma ya zama Ministan kudin kasar

Asali: Depositphotos
Kwanan nan mu ka ji ana rade-radin an cire Ministar kudin Najeriya watau Zainab Shamsuna Ahmed daga mukamin ta inda har wani babban gidan Talabijin na kasar watau TVC News ta rahoto wannan labari a farkon makon nan.
Yanzu labari ya zo mana daga Ma’aikatar kudin kasar cewa har yanzu Zainab Shamsuna tana nan a kan kujerar ta na Ministar na wucin-gadi. An nada Shamsuna wannan matsayi ne bayan Kemi Adoesun ta ajiye mukamin kwanaki.
KU KARANTA: Da duminsa: Kungiyar kwadago ta janye shiga yajin aiki, gwamnati za ta biya N30,000
Wani Hadimin Ministar kasar mai suna Musadiq Aruwa ya bayyana cewa labarin da ake yadawa na cewa an sauke Ministar daga kujerar ta ba gaskiya. Aruwa ya bayyana wannan ne a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita.
Yanzu dai ta tabbata cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai maye gurbin Zainab Shamsuna da Udo Udoma kama yadda ake fada ba. Mista Udoma dai shi ne Ministan kasafin kudi kuma har yanzu yana nan a kan wannan kujerar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng