Yanzu-yanzu: Gwamna Lalong ya yiwa Buratai ta'aziyar rasuwar Janar Alkali
Gwamnan jihar Plateau, Mr Simon Lalong ya ziyarci shugaban hafsin sojojin Najeriya, Laftanat Janar Tukur Yusuf Buratai domin yi masa ta'aziyya game da rasuwar marigayi Janar Idris Alkali da aka kashe a Jos.
An gano gawar Alkali ne a wata tsohuwar rijiya a garin Dura-Du na jihar Plateau bayan an kwashe makonni ana nemansa.
Lalonga ya ziyarci Buratai ne a hedkwatan hukumar sojin Najeriya da ke Abuja a yau Litinin domin jajinta masa.
DUBA WANNAN: Fallasa: An gano yadda gwamnatin Buhari ta waske da N378bn
Anyi jana'izar Janar Alkali ne a ranar Asabar a makabartan Gadu da ke Abuja bayan an yi masa sallah a babban masallacin Abuja.
Legit.ng Hausa ta samu rahoton ziyarar da Lalong ya kai wa Buratai ne a shafin Twitter na hukumar sojin Najeriya @HQNigerianArmy.
Ga hotunan yadda ziyarar ta kasance.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: UGC

Asali: Twitter
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng