Ma’aikatan lafiya da na hanyoyi da na Makaranta za su tafi yajin aikin din-din-din
Mun samu labari cewa Ma’aikatan Najeriya da dama za su shiga yajin aiki a halin yanzu. Tuni dai har Kungiyoyin Ma’aikatan kasar sun fara shiryawa yajin da ake sa rai za a fara cikin tsakar daren yau.

Asali: Depositphotos
Kamar yadda labari ya iso mana, Kungiyoyin da su ka hada da na Ma’aikatan jiragen sama na NUATE, ATSSAN, NAAPE da ANAP za su shiga yajin aikin da Kungiyar kwadago ta yi kira a Ranar Talata 6 ga Watan Nuwamban nan.
Yanzu dai Kungiyoyin Ma’aikatan na Direbobin jirigin sama da sauran Ma’aikatan jirgi sun fitar da sanarwa cewa daga yau za su daina aiki a Kasar. Ma’aikatan za su fara yajin aiki ne saboda rashin karawa Ma’aikata albashi.
KU KARANTA: Yajin aiki ya jawowa wani kamfani asarar Miliyan 60 a Najeriya
Haka kuma Kungiyar nan ta Ma’aikatan da ke aiki a kwalejin ilmi da sauran Makarantun gaba da Sakandaren da ke da alaka da Jami’o’i sun ce ba za a bar su a baya ba. Ma’aikatan za su bi Kungiyar NASU da SSANU zuwa wannan yaji.
Kungiyar SSANU ta bakin wani Sakataren ta na Kaa Kwamared Kingsley U.S Okayi ta tabbatar da cewa ba za a bar ta a baya wajen wannan yaji ba. Kungiyar ta manyan Ma’aikatan Jami’a za ta bi Takwaran ta ASUU wanda tuni ta soma na ta yajin.
Kungiyar Ma’aikatan lafiya na kasar nan ita ma dai ta sanar da cewa ba za a bar ta a baya ba a wannan yajin aiki da Kungiyar kwadago ta shirya. Wani babban Jami’in Kungiyar na kasa Kwamared Musa Chara ya bada wannan sanarwa a jiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng