'Yan sanda sun ceto babban soja da aka sace, sun kama mutane 4
Jam'ian 'yan sanda, a jihar Delta, sun yi nasarar kubutar da jami'in sojin ruwa, Omoniyi D. Kola, tare da kama mutane 4 da ake zargi da sace shi.
An mutanen ne a yankin Ebada-Elume da ke karamar hukumar Sapele a jihar Delta.
CSP Anieteh Eyoh, shugaban ofishin rundunar 'yan sanda ta "C" da ke Asaba ne ya ya jagoranci jami'an 'yan sandan da su ka yi aikin kubutar da sojan da kuma kama mutanen da su ka sace shi.

Asali: UGC
Sai dai duk da an kama 4 daga cikin wadanda su ka sace sojan, jagoransu ya samu damar tserewa.
DUBA WANNAN: Ni ne na kafa APC, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar
Tuni Eyo ya mika mutanen da ya kama ga ofishin 'yan sanda na Sapele.
Rahotanni sun bayyana cewar yanzu haka jami'in sojin da aka kubutar na samun kulawa a asibitin sojojin ruwa da ke Effurun, karamar hukumar Uvwie a jihar Delta.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Delta, Muhammad Mustafa, ya tabbatar da rahoton kubutar da jami'in da kuma kama wadanda ake zargi da kama shi.
"Jam'ian 'yan sanda sun kewaye yankin da mutanen da ake nema su ka buya a yankin Sapele. Yanzu haka jami'in sojin na samun kulawa a asibitin sojojin ruwa da ke Effurun yayin da mu ke cigaba da bincike," a cewar Mustafa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng