Nifa aikin Allah nake fi-sabililahi a NHIS - Dakataccen shugaban hukumar
- An kafa kwamiti na mutum Bakwai domin suyi binceka akan shugaban NHIS
- Yace yana rike da mukamin ne saboda yayi aiki don Allah
- Tunda aka fara binciken baibar aikinsa ba

Asali: Depositphotos
Shugaban NHIS Prof Usman Yusuf yace yana rike da mukamin sa ne saboda yana aikin sa don Allah.
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai kafin ya samu sakon ajjiye aiki na wani lokaci daga wajen Gwamnatin tarayya.
Gwamnatin ta kafa kwamiti na mutane Bakwai bisa ga zargi da ake masa wanda hakan shiya zanyo aka bashi hutu daga aiki.
Yusuf yace tun da aka fara gudanar da bincike a kansa a 18 ga watan October baibar aikin sa ba,yanaci gaba da aikin sa yayin da suma kwamiti suke nasu aikin.
DUBA WANNAN: A daina kisan gilla a Najeriya
Ya bayyanawa yan jarida cewa a baya abin yana damunsa idan akace ya sace wannan ya sace wancan wanda har baya iya tafiya da takaddar gida saboda matarshi tana shiga damuwa .
Amma zuwa yanzu ba abinda yake damuna saboda nasan inayin aikina tsakani da Allah.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng