Zan kara inganta habakar tattalin arzikin Najeriya - Buhari
Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito mun samu cewa, a yau Alhamis shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin sake inganta habakar tattalin arzikin Najeriya domin cin riba da kuma jin dadin al'ummar kasar nan.
Cikin wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasa Mista Femi Adesina ya bayyana, shugaban kasa Buhari ya sake jaddada aniyyarsa gami da daura damarar nisanta kasar nan akan Tudun tsira tare da mika ta zuwa ga gaci.
A cewarsa, "ko shakka ba bu tattalin arzikin kasar nan na da kyawu a halin yanzu amma za mu sake jajircewa domin inganta habakarsa."
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin karrama sabbin jakadun kasashen Pakistan, Senagal da kuma na Belarus zuwa Najeriya, inda ya neme su kan inganta dankon zumunta da kuma kyakkyawar alaka a tsakanin kasashen.

Asali: Depositphotos
Jagoran na Najeriya yayin ganawa da sabon jakadan kasar Pakistan, Manjo Janar Waqar Kingravi mai ritaya, ya yabawa kyakkyawar dangantarka ta tsaro dake tsakanin kasashen biyu da a halin yanzu kowace ke ribatar tasirin hakan.
KARANTA KUMA: Bulalar Sharo ta salwantar da rayuwar wani Bafulatani a jihar Jigawa
Kazalika shugaba Buhari yayin karrama sabon jakadan kasar Senegal, Mista Babacar Ndiaye, ya yabawa shugaban kasa Macky Sall dangane da jajircewar tare da taka muhimmiyar rawar gani kan harkokin siyasar kasar Guinea Bissau.
Yayin ganawa kuma da sabon jakadan na kasar Belarus, Mista Vyacheslav Beskosky, shugaba Buhari ya jaddada tsayuwar dakansa wajen inganta habakar tattalin arziki inda yabawa kasar dangane da kyakkyawan karamci ga Daliban Ilimi dake gudanar da karatuttukansu can kasar dake Gabashin nahiyyar Turai.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng