Harkar kasuwanci: Dangote ya kafa ranar koyon tuyan fanke na Duniya

Harkar kasuwanci: Dangote ya kafa ranar koyon tuyan fanke na Duniya

Mun samu labari daga Jaridar Punch cewa Attajirin nan na Nahiyar Afrika Aliko Dangote wanda shi ne Shugaban Kamfanonin Dangote yana kokarin kawo wani sabon tsari a fannin kasuwancin fulawa.

Harkar kasuwanci: Dangote ya kafa ranar koyon tuyan fanke na Duniya
Kamfanin Dangote zai koyawa mutane soye-soyen kayan fulawa
Asali: Depositphotos

Babban Attajirin nan da ake ji da shi a Najeriya ya kafa ranar fanke ta Duniya inda kowa zai fito ya baje kwarewar sa wajen tuyar fanke. Za a rika yin wannan gasa ne a kowace Ranar 27 ga watan Oktoba kamar yadda kamfanin Dangoten su ka bayyana.

Sunan wannan tsari dai “World Puff-puff Day” inda za ayi amfani da har ton 2 (watau manyan buhuna 50 masu kilo 40) na garin fulawa wajen yin toye-toyen fanke. A wannan rana za a soya fanke 30, 000 inji wata Jami’ar Kamfanin fulawa na Dangote.

Misis Funmilayo Bolarinwa wanda ita ce Shugaban harkar kasuwanci na Kamfanin fulawan na Dangote tace su na sa ran doke tarihin da aka taba kafawa har ya shiga littafin nan na Guinness Book na tuyan kilo 200 (watau manyan buhuna 4) na fulawa.

KU KARANTA:

Shugaban Kamfanin na Fulawa watau Halima Dangote tace za su rika kawo wadanda su ka kware wajen tuya da soye-soyen sarrafa fulawa domin koyawa jama’a yadda ake hada irin su Burodin kwalama na zamani da sauran su domin al’umma su karu.

Za a yi kokari wajen ganin an koyawa jama’a soya fanke wanda aka fi sani da Turanci da puf-puf. Gidajen mutane da-dama za su koyi yadda ake tuyar wannan kaya na kwalama a karkashin kamfanin Fulawan Dangote inji wani babba a Kamfanin.

Wannan tsari dai zai taimakawa Jama’a a Kasar kwarai da gaske domin kuwa fanke yana cikin abincin da jama’a su ka fi nema farat daya idan su na jin yunuwa ko kuma kwadayi ko kuma ‘yar sha’awa na marmari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng