'Yan dabar siyasa sun kashe Baraden Sunnah a Sokoto
Wasu gungun matasa da ake zargin 'yan dabar siyasar APC ne sun kashe wani dan-gani-kashenin jam'iyyar PDP mai suna Abu Kalhu da aka fi kira da Baraden Sunnah a Sokoto.
Ana zargin wani jigo a jam'iyyar APC da aika 'yan dabar domin su kashe Baraden Sunnah.
A cewar wasu shaidar gani da ido, an kawo 'yan dabar kimanin su 40 a cikin wasu motoci biyu kirar Toyota Hilux har gidan Baraden Sunnah da ke unguwar Kofar Kade da misalin karfe 9:00 na daren ranar Talata.
'Yan dabar sun datse dukkan hanyoyin da ke zuwa gidan Baraden Sunnah yayin da wasu daga cikinsu su ka fito da shi daga gidansa su ka caccaka ma sa wuka a ciki har sai da ya mutu.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: Jigo a APC ya yi murabus bayan ya zargi gwamnati da almundaha
"Ai asali yaransa ne kafin ya koma PDP. Mu na zargin wasu manyan 'yan siyasa da hannu a kisan shi saboda ya ki shiga jam'iyyar su," kamar yadda wani aboki ga marigayin ya shaidawa jaridar Daily Trust.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar 'yan dabar sun jiwa wani dan uwa ga marigayin ciwo, amma yanzu yana samun kulawa a asibiti.
Sakataren yada labaran jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, Abdullahi Hausawa, ya yi Alla-wadai da kisan Baraden Sunnah tare da yin kira ga jami'an tsaro da su dauki matakan ladabtar da duk ma su hannu a kisan.
Da aka tuntubi kakakin jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Bello Yusuf Danchadi, ya ce babu ruwan jam'iyyar APC da batun kisan.
Kokarin jin ta bakin kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Sokoto, DSP Cordelia Nwewe, kafin buga wannan rahoto bai samu ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng