Har yanzu akwai Mahandama masu rike da dukiyar Kasa - Shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi fusatattun jam'iyyarsa ta APC kan cewa su yi taka tsan-tsan yayin kada kuri'un su domin kuwa har yanzu akwai ragowar mahandama ma su rike da dukiyar al'ummar kasar nan.
Cikin wata sanarwa da sa hannu kakakin shugaban kasa Mista Femi Adesina, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin wata liyafar dare tare da 'yan takara da mambobin jam'iyyar APC da ya dauki nauyin shiryawa a fadarsa ta Villa dake birnin tarayya na Abuja a ranar Talatar da gabata.
Shugaba Buhari yake cewa, "har ila yau akwai ragowar mahandama masu rike da tarin dukiya mai dumbin yawa da suka tatsi dukiyar talakawan kasar nan tun a lokutan baya".
A sanadiyar haka shugaba Buhari yake kira ga 'yan takara na jam'iyyarsa kan cewa su yi taka tsan-tsan tare da tantance ra'ayoyi da zabin su yayin kada kuri'u a kasar nan domin tabbatuwarta zuwa ga tudun tsira na ga hannun masoya da kuma masu kishin ta.
Shugaba Buhari ya horesu kan riko da gaskiya gami da nagarta ta adalci a duk wani mataki na jagoranci da suka tsinci kawunan su.
KARANTA KUMA: Makiyaya sun hallaka wata babbar Gonar Shinkafa a jihar Taraba
Kazalika shugaban kasar ya gargade su kan riko da akida ta kishin kasa da kuma kawo managarcin sauyi a matsayin manufa ta neman takarar kowace kujera da madafan iko.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya Talata shugaban kasa Buhari ya shiga bayan labule tare da wasu gwamnoni hudu na jam'iyyar adawa ta PDP a fadarsa ta Villa dake garin Abuja.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng