Makiyaya sun hallaka wata Babbar Gonar Shinkafa a jihar Taraba

Makiyaya sun hallaka wata Babbar Gonar Shinkafa a jihar Taraba

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, makiyaya rike da makamai tare da Dabbobin su sun hallaka wata wawakekiyar Gonar Shinkafa mallakin kamfanin Wal-Wanne Nigeria a kauyen Dubale dake karamar hukumar Lau ta jihar Taraba.

Jagoran wannan kamfani na manoma, Muhammad Musa, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawarsa da manema labarai ya Laraba cikin babban birnin Jalingo.

Mista Musa ya bayyana takaicinsa dangane da wannan mummunan lamari sakamakon kyakkyawar yabanya da gonar ta yi kuma ke daf da girbi yayin da Makiyaya da kimanin Dabbobi sama 200 sun dira tare da hallaka ta.

Ya nemi hukumomin tsaro kan kawo ma su agaji wajen cafke wannan miyagun makiyaya tare da hukuntasu domin ya zamto izina ga masu hali makamancin na su.

Makiyaya sun hallaka wata Babbar Gonar Shinkafa a jihar Taraba
Makiyaya sun hallaka wata Babbar Gonar Shinkafa a jihar Taraba
Asali: Depositphotos

Mista Musa ya kuma nemi gwamnatin jiha da ta tarayya kan kawo masu dauki na tallafi dangane da wannan mummunan lamari da ya janyo koma baya ga fatan su na kasancewa cikin sahun zakarun noma a wannan shekara cikin kasar nan.

KARANTA KUMA: Za mu kawo karshen zangar-zangar 'Kungiyar Shi'a a Najeriya - Sufeton 'Yan sanda

A yayin tuntubar shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen Arewa maso Gabashin Najeriya, Mafindi Danburam, ya bayyana takaicinsa dangane da wannan lamari na kaico inda ya nemi hukumomin tsaro akan tashi tsaye domin cafke dukkanin masu hannu cikin wannan aika-aika.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Ribas, Ayodele Fayose, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kisan 'Yan Shi'a a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng