Abuja tayi Allah wada da kisan falastinawa har 58 masu zafin kai ga Israila

Abuja tayi Allah wada da kisan falastinawa har 58 masu zafin kai ga Israila

- Gwamnatin tarayya ta kushe kashe palasdinawa 58 da Isra'ilawa sukayi

- Dole ne gwamnatin Isra'ila ta rage amfani da karfi ga farar hula marasa makamai da kuma yara

- Mutane 1,000 ne suka samu raunuka a sakamakon karo da sukayi

Abuja tayi Allah wada da kisan falastinawa har 58 masu zafin kai ga Israila
Abuja tayi Allah wada da kisan falastinawa har 58 masu zafin kai ga Israila
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya ta kushe palasdinawa marasa makamai guda 58 da suka hadu da Isra'ilawa a yankin Gaza.

Ma'aikatar kula da harkokin waje ta bayyana damuwar Gwamnatin tarayya akan kisan.

"Dole ne gwamnatin Isra'ila tayi kokarin hana amfani da karfi ga farar hula marasa makamai, hadi da yara da kuma mutunta hakkin Dan adam na palasdinawa da kuma dokokin kasashen duniya", inji ma'aikatar.

DUBA WANNAN: Hanyoyin magance Shianci a Najeriya

Ofishin dillancin labarai yace ma'aikatar lafiya ta Gaza tace palasdinawa 58 aka kashe kuma kusan mutane 1,000 ne suka samu raunuka daban daban.

Jami'an tsaron Isra'ilawa sunce, sun maida martanin yunkurin gangancin da aka kawo musu ne tare da tsallake iyaka don kawo hari ga Isra'ila.

Sojin Isra'ila sunce uku daga cikin palasdinawa da aka kashe, an kama su ne suna kokarin daga abubuwa masu fashewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel