Sanata Bukar Abba ya debo ruwan dafa kansa kan furucin rashin nasarar Buhari a Arewa maso Gabas

Sanata Bukar Abba ya debo ruwan dafa kansa kan furucin rashin nasarar Buhari a Arewa maso Gabas

A ranar Litinin din da ta gabata ne Sanata Bukar Abba Ibrahim ya fahimci kuskuren sa kan furuci da hasashensa na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyarsa ta APC ba za su yi nasara ba a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan yayin babban zabe na 2019.

Kamar yadda wani dan majalisar wakilai Goni Bukar Lawan ya zayyana, furucin Sanata Bukar ba ya da nasaba ko ta sisin kobo ga jihar sa ta Yobe ko kuma ilahirin yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sai dai Sanata Bukar ya musanta furta wannan kalami da ake zarginsa da bayyanawa a karshen makon da ta gabata cikin birnin Abuja yayin kaddamar da littafin sa cikin wani bangare na murnar cikarsa shekaru 70 a doron kasa.

Sanata Bukar Abba ya debo ruwan dafa kansa kan furucin rashin nasarar Buhari a Arewa maso Gabas
Sanata Bukar Abba ya debo ruwan dafa kansa kan furucin rashin nasarar Buhari a Arewa maso Gabas
Asali: Depositphotos

Cikin wata sanarwa da sa hannun kakakinsa, Yusuf Ali ya bayyana cewa, Sanata Bukar ba ya da wata danganta da wani kalami na cewa magudin zabe na kololuwa ba zai tseratar da shugaba Buhari da kuma jam'iyyarsa ta APC.

KARANTA KUMA: Ina bukatar wani karon domin kawo sauyi a Najeriya - Buhari

Kazalika Kakakin ya nesanta Ubangidansa da kalami na cewar duk wani tsanani na jam'iyyar adawa ta PDP bai ko kama kafar na jam'iyyar APC ba kamar yadda ake zargin Sanatan da furtawa baya ga fafutika gami da jajircewarsa ta kubutar da kasar nan daga hannun jam'iyyar ta PDP.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira a jihar Kaduna domin ganawa da dukkanin masu ruwa da tsaki kan tashin-tashinar dake faman aukuwa a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel