Uwargidar Hameed Ali ta bar Duniya tana da shekaru 53
Wani labari mai ban takaici ya iso gare mu na rasuwar Iyalin Shugaban Hukumar kwastam na kasa baki daya watau Kanal Hameed Ali mai ritaya. Hadiza Jummai Ali ta cika ne a jiya Litinin 29 ga Watan Oktoba.

Asali: Facebook
Hajiya Hadiza Jummai Ali ta bar Duniya ne tana da shekaru 53 da haihuwa. Za a bizne Matar Shugaban Hukumar kwastam na kasar yau da karfe 8:00 na safe. Za a kuma yi sallar Jana’iza ne a babban Masallacin nan na Annu da ke Abuja.
Jami’in da ke magana da yawun bakin Hukumar gidan kwastam na Najeriya PPRO Joseph Attah ya tabbatar da rasuwar wannan Baiwar Allah. Attah yace babu shakka Iyalin wannan mata sun yi rashi babba wanda sam ba zai misaltu ba.
KU KARANTA: Saboda nace Buhari mugu ne aka kama ni aka daure - Metuh
Hadiza Jummai Ali ta taba zama Uwargidan Jihar Kaduna a lokacin da Kanal Hameed Ali yayi Gwamna a mulkin Soja na Gwamnatin Janar Sani Abaacha na tsawon shekaru 2 daga Watan Agustan 1996 har zuwa karshen shekaran 1998.
Kamar yadda Jaridar Leadership ta bayyana, Hajiya Hadiza Ali ta haifi ‘Ya ‘ya 4 da Kanal Hameed Ali wanda yanzu duk su na raye. Asalin Ali dai mutumin Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng