Babban jirgin sama makare da fasinjoji ya fada cikin ruwa, kowa da kowa ya mutu
Hotuna sun fara bayyana dangane da wani babban jirgin sama JT-610, wanda ya gamu da hatsari a kasar Indonesia jim kadan bayan tashin yayin da yake cike makil da fasinjoji, a lokacin daya nufi Pangkal Pinang, wani tsibiri dake Arewacin Indonesia.
Majiyar Legit.com ta ruwaito kafin jirgin ya tashi sai da matukinta, wani dan kasar Indiya, Bhavye Suneja ya bayyana ma shuwagabanninsa cewa jirgin na da matsala, sai suka ce masa ya koma filin jirgin daya tashi, a hanyarsa ta komawa ne sai ya bace daga na’urar sarrafa jirage, ashe ya tujuma cikin teku.
KU KARANTA: Batun takardun karatun Buhari ya bar baya da kura: Karanta abinda kundin tsarin mulki yace

Asali: Depositphotos
Sai dai har yanzu mahukunta sun gagara gano bakin zaren, dalili kuwa shine, jirgin nan sabo ne, kuma yanayin garin babu hazo, rana ake yi, kuma matukin jirgin kwararre ne, don haka basu ga ta yadda jirgin zai yi hatsari ba
Wannan mummunan hatsari ya janyo asarar rayukan mutane 189, kusan kowa da kowa dake cikin jirgin yam utu, daga cikinsu akwai wani matashi mai shekaru 22, Deryl Febrianto wanda duka sati biyu kenan da yin aurensa, kamar yadda matarsa Lutfinani Eka ta bayyana.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na kasar, Bambang Surayo ya bayyaa cewa “Ina ganin babu wanda ya rayu a cikin fasinjoji 189, wadanda muka gano, mun samesu jikkunansu sun guntule, don haka akawai yiwuwar sun mutu duka.”
An samu wani mutumi da Allah yayi ma gyadar dogo, Sony Setiawan, wanda ya kamata yabi jirgin, amma cincirindon ababen hawa ya rike shi akan hanyarsa ta zuwa filin sauka da tashin jiragen, da haka ya bata lokaci har jirgin ya tashi, inda bayan mintuna 13 ya tunjuma cikin teku.
A wani labarin kuma, mamalakkin kungiyar kwallon kafa ta Leicester dake fafatawa a gasar kwallon kafa ta Premier League, Vichai Srivaddhanaprabha ya rasu a ranar Asabar, 27 ga watan Oktoba a hadarin jirgin sama mai tashin angulu, jim kadan bayan ya kammala kallon kwallo.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng