Zargin cin hanci: Aminu Daurawa yayi kira ga Majalisa ta yi bincike ta hukunta mai laifi
Yayin da ake cigaba da hurowa Gwamnan Jihar Kano wuta game da zargin karbar cin hanci na Dalolin kudi, wasu Malamai sun yi huduba game da batun wanda wannan sam bai yi wa Gwamnatin Kano dadi ba.

Asali: UGC
Yanzu haka mun samu labarin duk abubuwan da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya fada a hudubar sa wanda ake kishin-kishin din ta jawo masa fushin Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje a karshen makon da ya wuce.
A Juma’ar da ta wuce ne Shugaban Kungiyar Hisbah ta Kano, Aminu Ibrahim Daurawa yayi magana game da zargin da ke wuyan Gwamna Abdullahi Ganduje inda yayi kira ga Majalisa tayi bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
Malamin yace idan har sharri da kage aka yi wa Gwamna, to ba za zai kunyata ba illa ma ya kara kima da daraja a gaban jama’a tare da kuma tonawa ‘Dan Jaridar da yayi wannan aiki asiri na yunkurin batawa Mai Girma Gwamna suna.
KU KARANTA: Bidiyon karbar daloli: Gwamna Ganduje ya garzaya kotu
Shehin Malamin ya kara da cewa idan kuma har Gwamnan ya karbi wadannan kudi na rashawa, to ya zama wani babban abin kunyan da ba a taba ganin irin sa a Jihar Kano ba. Daurawa yace idan aka hukunta Gwamna, kowa zai shiga taitayin sa.
Sheikh Aminu Daurawa ya nuna cewa ya kamata gaskiya tayi halin ta a wajen wannan bincike ganin yadda wannan Gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari ta shelantawa Duniya shirin ta na yakar cin hanci da rashawa a Najeriya.
KU KARANTA: Ba mu da wani banbanci da Jam'iyyar PDP - inji Sanatan APC
Aminu Daurawa ya kuma bayyana cewa idan har Hukuma ba tayi komai game da wannan batu ba, hakan zai batawa Gwamnatin Buhari suna tare da kuma nuna cewa ba da gaske ake yi wajen yaki da cin hanci da rashawa a cikin Kasar ba.
Babban Malamin ya kuma lissafo wadanda aka kama aka hukunta a bisa zargin cin hanci da rashawa da satar kudin Jama’a wadanda su ka hada da irin su tsohon Gwamna a Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau wanda ake gani da mutunci.
Daurawa yace nan gaba jama’a za su rika tsoron karbar mulki idan har aka hukunta maras gaskiya a wannan bincike da Majalisar dokoki ta ke gabatarwa. Wannan ne dai ya sa Gwamna Ganduje ya aikawa Gwamnan sammaci bayan hudubar.
Asali: Legit.ng