Leah Sharibu: 'Yan Boko Haram sun sa kudin fansa Naira Biliyan 100

Leah Sharibu: 'Yan Boko Haram sun sa kudin fansa Naira Biliyan 100

Dazu nan mu ka samu labari cewa ‘Yan ta’addan Kungiyar Boko Haram su na neman makudan Biliyoyin Naira kafin su saki Leah Sharibu wanda su ka sace kwanaki a cikin Garin Dapchi da ke Jihar Yobe.

Leah Sharibu: 'Yan Boko Haram sun sa kudin fansa Naira Biliyan 100
Gwamnati tayi wa Iyayen Leah Sharibu alkawarin ceto Diyar su
Asali: UGC

Ana kishin-kishin din cewa bangaren ‘Yan Boko Haram da su ke tsare da Leah Sharibu sun nemi a bada Naira Biliyan 100 kafin su saki wannan yarinya. Gwamnatin Shugaba Buhari dai tayi alkawarin ceto wannan Baiwar Allah tun kwanaki.

Sai dai Majiyar ta mu ta bayyana cewa idan har Gwamnati ta bada wannan kudi, ‘Yan ta’addan za su sayo manyan makamai ne wanda za su cigaba da ta’adi a kasar. Wannan ya sa Gwamnati ta ke gudun ba ‘Yan ta’addan abin da su ke bukata.

Jaridar Punch tace Gwamnati na gudun mikawa ‘Yan ta’addan irin wannan makudan kudi wanda a karshe za su kare wajen makamai a kuma cigaba da kai munanan hari a Najeriya a daidai lokacin da ake shiryawa babban zaben kasar a 2019.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe shanun wasu Bayin Allah

Kwanaki ne ‘Yan Boko Haram su ka sace ‘Yan mata 110 a wata Sakandare a cikin Jihar Yobe. Daga baya an dawo da yara 104 inda aka tabbatar da cewa yara 5 sun rasu yayin da aka rike Leah Sharibu saboda ta ki karbar addinin Musulunci.

‘Yan Boko Haram dai sun sha alwashin cewa ba za su kashe Sharibu ba, amma sun ce za sy maida wannan yarinya Baiwar su. Shugaban kasa Buhari yayi wa Iyayen wannan karamar yarinya alkawarin cewa za ta dawo gida kwanan nan.

Dazu kun ji cewa an gano yara 57 daga cikin ‘Yan matan nan na Chibok da ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka sace shekarun baya. An ga yaran ne yanzu a cikin wani Kauye a Kamaru mai makwabtaka da Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng