Mustapha Atiku ya bayyana muhimman bayanai a kan mahaifinsa
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, na sadaukar da lokaci domin inganta rayuwar iyalinsa ta hanyar koyar wa tare da saka su a cikin harkokin kasuwancinsa da za su gada, kamar yadda dansa ya bayyana.
Mustapha Atiku Abubakar, da ga Atiku Abubakar, ne ya sanar da hakan a jiya juma'a, a shafinsa na Tuwita.
Mustapha ya bayyana yadda ya kasance cikin irin taron duk shekara da Atiku ke shiryawa iyalinsa tun yana da shekaru 12 da haihuwa.
Mustapha na wadannan ne a matsayin raddi ga wani Henry Okelue bayan ya zargi Atiku da daina neman wani ilimi a cikin shekaru 49 da su ka wuce.

Asali: Facebook
Mustapha ya yi bayanin yadda mahaifinsa ke ilimintar da kansa da iyalinsa domin ganin inganta rayuwar sa da ta iyalinsa tare da kokarin koya ma su dabarun neman kudi domin dogaro da kai.
DUBA WANNAN: Sanata Shehu ya bayyana makiyan Najeriya na zahiri
"Ina da shekaru 12 lokacin da na fara raka mahaifina aji domin daukan darasi. Duk shekara sai mahaifinmu ya gayyato manyan Farfesoshi domin su ilimantar da mu. Tsawon shekaru 10 kenan yanzu ina halartar irin wannan ajin daukan darasi da mahaifin mu ya farlanta duk 'ya'yansa halarta," in ji Mustapha.
Daga cikin irin masana da Mustapha ya lissafa sun taba gabatar da lakca a daya daga cikin ajin iyalin Atiku akwai Farfesa Gimeno na kasar Spain da babban lauyan Najeriya, Eyitayo Jegede.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng