An Shiga Tashin Hankali da Rigima Ta Kaure tsakanin Matasa a Jihar Kaduna
- An shiga tashin hankali sakamakon rikici tsakanin wasu gungun matasa a unguwannin Kwaru da Unguwar Yero da ke jihar Kaduna
- An ce mutum uku sun samu raunuka a rikicin farko, yayin da ɗaya daga cikinsu ya rasu daga baya
- Rundunar ’Yan sanda, DSS da jami’an MOPOL sun kai dauki yankuan da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - An shiga fargaba bayan wasu gungun matasa masu hamayya da juna sun yi arangama a unguwannin Kwaru da Unguwar Yero da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna.
Rikicin, wanda rahotanni suka ce ya jikkata wasu mutane, ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin matasan unguwannin biyu kusan mako guda da ya gabata.

Source: Original
An ce ɗaya daga cikin matasan da suka jikkata daga Unguwar Yero ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a rikicin farko, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Matasa sun yi arangama a Kaduna
Hakan ne ya fusata abokansa, waɗanda ake zargin sun yi yunƙurin ɗaukar fansar mutuwarsa a ranar Laraba.
Wani mazaunin Kwaru mai suna Sule ya ce lamarin ya haddasa fargaba a tsakanin mazauna yankin, har wasu ɗalibai suka tsere daga makarantunsu.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe, lokacin da ya ji hayaniya sannan ya fito domin ganin abin da ke faruwa, inda ya tarar da wasu matasa suna jifan juna da duwatsu.
“Wasu matasa daga Kwaru da Unguwar Yero sun samu saɓani kusan mako guda da ya wuce, inda wani matashi ya ji rauni kuma daga baya ya rasu.
“Yau Laraba, bayan yara sun tafi makaranta, sai muka fara jin hayaniya. Da na fito, sai na ga mutane sun taru, yayin da wasu ke jifan juna da duwatsu tsakanin matasan Unguwar Yero da wasu mazauna Kwaru da suka je makabarta,” in ji shi.
Sule ya ce lamarin ya ƙara tayar da hankula a tsakanin mazauna yankin, yana mai cewa unguwannin biyu sun taɓa fuskantar irin wannan saɓani a baya kafin daga bisani aka samu ɗan zaman lafiya.
Ya tabbatar da cewa jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ’yan sanda da rundunar ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL), tare da sauran jami’an tsaro, sun isa yankin domin dawo da zaman lafiya.

Source: Getty Images
’Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun shawo kan matsalar bayan tura jami’ai da dama zuwa yankunan.
“Lamarin yana ƙarƙashin kulawa bayan tura jami’an tsaro da dama zuwa unguwannin,” in ji shi.
Rikici ya yi ajalin mutane a Neja
Kun ji cewa akalla mutane uku sun jikkata a wani rikici da ya auku tsakanin manoma da makiyaya a yankin Kataeregi da ke karamar hukumar Katcha a jihar Neja.
Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa jami'an tsaro sun yi nasarar kwantar da tarzomar tare da tabbatar da tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng

