Biyafra ta bayyana yaudarar da ta yi zargin Atiku na shiryawa 'yan kabilar Igbo
Kungiyar gamayyar kungiyoyin dake fafutikar kafa kasa Biyafra (Biafra Nations League, BNYL,) ta ce dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai yi amfani ne kawai da 'yan kabilar Igbo domin cimma burinsa.
Kungiyar ta gargadi 'yan kabilar Igbo da su guji goyon bayan Atiku ko yi masa yakin neman zabe saboda kawai ya zabi mataimaki daga yankin su.
A wani jawabi da daya daga cikin wadanda su ka kafa kungiyar kuma mataimakin shugabanta, Ebuta Ogar Takon, ya aike ga manema labarai, ya ce kungiyar ba ta da wani dan takara tare da fadin cewar su kishin Biyafra ne kawai a ransu.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa
Takon ya gargadi 'yan jam'iyyar APC da kar su dauki matsayar da kungiyar ta dauka tamkar goyon baya ne ga dan takarar su, tare da bayyana cewar, "babu wani canji da Atiku ko Buhari za su kawowa Najeriya."
Sannan ya kara da cewa, "Atiku da Buhari 'yan uwa ne domin dukkansu daga arewa su ka fito. Sun dauki mataimaka ne daga kudu don su cigaba da wasa da tunanin mu. Akwai bukatar ma su goyon bayansu daga kudu su bude idanunsu sosai.
"Za a kara yin amfani ne kawai da 'yan kabilar Igbo idan su ka bari Atiku ya yaudare su da batun zaben mataimaki daga yankin kudu maso gabas.
"Abun tambaya a nan shine da gaske ne Atiku zai iya yiwa tsarin mulkin Najeriya garambawul idan an zabe shi?
"Mutanen yankin kudu maso gabas da na kudu maso kudu za su iya fita domin cigaba da kada kuri'a ga 'yan arewa," a cewar Takon.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng