Wani Wanzami ya murkushe budurwa 'yar 14 a jihar Legas
Mun samu rahoton cewa, a can jihar Legas hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta cikwikwiye wani matashin wanzami mai shekaru 18, Bakare Isma'il, da laifin yiwa wata budurwa 'yar shekara 14 fyade dake makotaka da shi.
Bakare ya yaudari wannan Budurwa har gidan Mahaifansa dake kan hanyar Banjo a yankin Ikorodu da misalin karfe 4.00 na yammacin ranar 13 ga watan Oktoba.
Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito sun bayyana cewa, Bakare ya bai wa wannan Budurwa abin sha mai kunshe da maganin bacci da bayan wasu 'yan lokuta ta lafke.
Jaridar ta ruwaito cewa, Bakare ya biya bukatarsa da wannan Budurwa mai sunan Bidemi inda farkawarta ke da wuya ta tsinci kanta jina-jina cikin jini.

Asali: Facebook
Wannan lamari ya sanya aka yi gaggawar shigar da korafi har gaban hukumar 'yan sanda da ba bu wata-wata Bakare ya shiga hannu inda ya musanta wannan zargi dake kansa.
KARANTA KUMA: 2019: Saraki, Atiku, Secondus, Obi sun tafi dauro damara a Dubai
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, an gurfanar da Bakare gaban kotun Majistire bisa wannan zargi na laifi da ya sabawa sashe na 137 cikin dokokin jihar Legas.
Alkaliyar kotun Misis O. Sule Hamza, ta bayar da umarnin garkame wannan Matashi a gidan kaso inda ta daga sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Dasumba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng