2019: Yarabawa sunyi kaca-kaca da Fashola kan yiwa Buhari kamfe

2019: Yarabawa sunyi kaca-kaca da Fashola kan yiwa Buhari kamfe

- Kungiyar Yoruba Youths Council tayi kaca-kaca da Fashola kan cewar yarabawa su zabi shugaba Buhari

- Kungiyar ta ce shugaba Buhari ba tabbuka wani abin azo a gani ba da har za su sake jefa masa kuri'unsu

- Har ila yau, Kungiyar ta ce sauya tsarin rabon arzikin kasa ne kawai zai magance matsalolin da ke addabar Najeriya

Wata kungiyar matasan Yarabawa sunyi Allah wadai da kalaman da aka ce Ministan Lantarki, Aiki da Gidaje, Mr Babatunde Fashola ya ce fadi inda ya bukaci al'ummar yankin Kudu maso Yamma su sake zaben shugaba Muhammadu Buhari.

2019: Yarabawa sunyi kaca-kaca Fashola kan yiwa Buhari kamfe
2019: Yarabawa sunyi kaca-kaca Fashola kan yiwa Buhari kamfe
Asali: Depositphotos

A jawabin da ya yi wajen wani taron jin ra'ayin al'umma, Fashola ya yi kira ga mutanen Kudu maso Yamma su zabi shugaba Muhammadu Buhari a 2019 muddin suna son mulki ya dawo yankin a 2023.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

Kungiyar mai suna Yoruba Youths Council ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari bai tabbuka wani abin azo a gani ba saboda haka bai cancani samun kuri'un yarabawa ba. Kungiyar ta yi tir da kalaman Fashola.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Eric Oluwole ya fitar a jiya Juma'a, ya bayyana cewar shugaba Buhari ba zai iya magance matsalolin da ke addabar Najeriya ba. Ya ce sauya tsarin rabon albarkatun kasa ne kawai zai kawo cigaba a kasar.

Kungiyar ta tunatar da Fashola cewar ya taba fadin cewar zai magance matsalar rashin wutan lantarki a Najeriya cikin watanni shida amma gashi yanzu ya yi shekaru uku a mulki kuma ya gaza magance matsalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164