Hatsarin Jirgin Ruwa ya salwantar da rayukan Mutane 11 a jihar Benuwe
Hukumar kula da kiyaye tashoshin jiragen ruwa ta NIWA, National Inland Waterways Authority, a yau Juma' ta bayar da tabbacin adadin rayukan Mutane 11 da suka salwanta a sanadiyar wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Benuwe.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, shugaban hukumar, Tayo Fadile yayin ganawa da manema labarai ya bayyana cewa, hukumar ta samu nasarar ceto Mutane 12 yayin laluben wasu Mutane 7 ke ci gaba da gudana.
Mista Fadile yayin ganawarsa da manema labarai ya alakanta aukuwar wannan tsautsayi a sanadiyar makire jirgin ruwan da adadin fasinjoji da ya sabawa ka'ida.

Asali: Depositphotos
Hukumar ta kuma yi karin haske sabanin wasu rahotanni da suka bayyana adadin rayuka 18 da suka salwanta a Kogin Buruku dake jihar Benuwe, inda ta bayar da tabbacin adadin rayuka 11 da suka salwanta.
KARANTA KUMA: Abba Kyari ya shiga ganawar sirrance da Shugaban hukumar INEC
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wata jaridar tattalin arziki ta duniya, The Economist, ta yi hasashen faduwar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin babban zaben kasa na 2019 da cewar tsohon mataimakin shugaban Atiku Abubakar zai yi galaba a kansa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng