Ministan sufurin Najeriya yayi kicibis da Gwamna Wike a Fatakwal
Mun samu labari cewa a jiya ne Gwamnan Jihar Nyesom Wike da Rotimi Amaechi wanda shi ne Ministan sufuri su ka hade a Garin Fatakwal a lokacin da Shugaban Kasa Buhari ya kai ziyara zuwa Jihar.

Asali: UGC
A jiya ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka da aka yi a babban filin jirgin saman da ke Garin Fatakwal a Jihar Ribas. Daga cikin Tawagar Shugaban kasar akwai wasu manyan Minstocin Najeriya.
Ministan sufuri na kasar wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi yana cikin wadanda su ka raka Shugaba Buhari zuwa Garin na Fatakwal inda aka kaddamar da ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta karasa.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta samar da karin wutar lantarki - Fashola
Yanzu dai tsohon Gwamna Rotimi Amaechi ba su shiri ko kadan da Magajin na sa watau Gwamna Nyesom Wike. Sai dai ziyarar da Shugaban kasar ya kai ta sa manyan ‘Yan siyasar sun yi gaba da gaba da juna ana ta yin muzurai.
Kwanan nan ne ma Rotimi Amaechi ya caccaki Gwamnatin Wike inda yace yanzu babu zaman lafiya a Jihar. Wannan ya sa Gwamnatin Jihar Ribas ta fadawa tsohon Gwamnan ka da ya sake shigowa Jihar idan har babu lafiyar tsaro.
Da farko dai Wike da Amaechi manyan Abokai ne a siyasa idan Wike ya rike Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnatin Ribas a lokacin Amaechi yana Gwamna. Sai dai Amaechi ya bata da Wike bayan ya zama Minista a lokacin Jonathan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng