Kisan janar Alkali: Mutanen da Sojoji ke nema ruwa a jallo sun mika kansu da kansu
Bayan akalla awanni 24 da rundunar yansandan Najeriya ta bayyana wasu mutane takwas dake da hannu cikin bacewar wani babban hafsan Soja, Manjo janar Ibrahim Alkali, sai ga wasu daga ciki sun mika kansu da kansu ga hukuma.
Majiyar LEGIT.com ta ruwaito a a ranar Juma’a 26 ga watan Oktoba ne mutane guda hudu suka mika kansa ga rundunar Yansandan jahar Filato dake garin Jos, daga cikinsu akwai dakacin garin Du Yakubu Rapp, shugaban matasan garin Matthew Rwang sai kuma Timothy Chuwang.
KU KARANTA: Muhimman ayyuka 4 da gwamnatin Buhari ta yi ma al’ummar jahar Kano
Idan za’a tuna a kwanakin baya ne rundunar Sojojin Najeriya ta kaddamar da aiki na musamman don ganin ta bankado inda janar Alkali ya shiga, inda suka dauki alwashin nemo gawarsa ko shi kansa idan yana da rai.

Asali: Twitter
Sai ga shi cikin ikon Allah Sojojin sun gano motarsda wasu kayayyakinsa a cikin wani rafi dake tsakiyar garin Du, a yayin da Sojojin ke gudanar da wannan bincike, daga nan ne rundunar Sojin a fara kama duk wani da bincike ya nuna akwai hannunsa cikin bacewar babban sojan.
Wata majiya mai ido ta tabbatar da cewar mutanen sun isa ofishin Yansandan ne da misalin karfe 10 na safe, tare da lauyansu, Mathew Godfree “Muna sa ido muga yadda Yansanda zasu dasu, idan suka kamasu suka daure, kaga sauran da ake nema ba zasu kawo kansu ba.
“Amma idan aka sallamesu, tabbas sauranma zasu kawo kansu zuwa sati mai zuwa.” Inji majiyar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng