Mahaifiyar Maryam Sanda ta gaza kai banten ta a hannun hukumar ICPC
- Har yanzu Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam Sanda tana tsare a hannun hukumar ICPC
- Rahotanni sun bayana cewar an bayar da belinta tun jiya Laraba amma ta gaza cika ka'idojin belin
Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam Sanda har yanzu tana tsare a hannun hukumar yaki da rashawa da laifuka masu alaka da rashawar (ICPC) tun bayan da aka kama ta a ranar Laraba da ta gabata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An gano cewar jami'an ICPC tare da 'yan sanda sunyi awon gaba da ita a wata fara mota kirar Toyota Hiace bayan ta fito daga babban kotun Abuja da ke Maitama a jiya inda ake cigaba da shari'ar kisar surukinta wanda ake zargin Maryam Sanda da wasu da hannu cikin kisar.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: Gasar karatun Al-Kur'ani: Dan asalin jihar Katsina ya bayar da mamaki a Saudiyya
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar an kama ta ne bayan ta ki amsa gayyatar da ICPC tayi mata na gurfana gaban alkali Nnamdi Dimgba na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja inda ta ce ba ta son mu'amala da ICPC.
Majiyar har ila yau ta bayyana cewar ICPC ta bawa Maimuna beli a yau Alhamis bayan ta kammala amsa wasu tambayoyi a ofishin hukumar misalin karfe 12.17 na ranar Laraba amma har yanzu tana tsare a hannun hukumar saboda ta gaza cika ka'idojin belin ta.
An gano cewar kotu ta bukaci ta gabatar da mutane biyu da ke aiki da gwamnatin tarayya wanda suka kai matsayi na 16 a aikin gwamnati kuma mazauna Abuja sannan kowannensu zai bayar da jinginan N10 miliyan goma kafin a sake ta.
Har ila yau kotun ta bukaci masu karbar belin su gabatar da takardan mallakar fili a Abuja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng