Duk mai son kwanciyar hankali, kar ya je kotu - Alkalin Alkalan Najeriya

Duk mai son kwanciyar hankali, kar ya je kotu - Alkalin Alkalan Najeriya

- Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen ya shawarci duk wanda ya ke son kwanciyar hankali ya guji zuwa kotu

- Justice Walter Onnoghen ya bayyana cewar an tsara kotu ne domin ta gano mai gaskiya da mara gaskiya

- Ya shawarci duk wanda ke son kwanciyar hankali ya nemi yin sulhu ba tare da zuwa kotu ba

Duk mai son kwanciyar hankali kar ya je kotu - Alkalin Alkalan Najeriya
Duk mai son kwanciyar hankali kar ya je kotu - Alkalin Alkalan Najeriya
Asali: Depositphotos

Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Nkanu Onnoghen ya bayyana cewar irin tsarin da akayi wa kotuna da bangaren shari'a ba tsari ba ne wanda zai faranta wa kowa rai.

Justice Onnoghen ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan batun fitar da tsarin yin sulhu ba tare da zuwa kotu ba wanda a taron shekara-shekara da Kungiyar Kwararrun Masu Sulhu na Najeriya suka gudanar a yau Alhamis.

DUBA WANNAN: Wata mace ta yi karar mijinta a kotu bisa gazawarsa wajen biya mata hakin kwanciyar aure

A cewarsa, "Na yi aiki da kotu da kuma sulhu irin na gargajiya kuma ina son in tabbatar muku cewar ba a tsara kotu domin ta kwantar wa kowa da hankali ba. Duk mai son kwanciyar hankali ya guji kotu."

"Domin muddin aka shiga kotu dole sai an samu mai gaskiya da mara gaskiya. Muna kallon hakokin mutane da nauyin da ya rataya a kansu. Ba tsari bane wadda zai tabbatar da kwanciyar hankali."

Amma idan mutane biyu da suka samu rashin jituwa suka fita daga kotu domin yin sulhu ba tare da ka'idojin da aikin shari'a ke aiki da shi ba, hankulan mutane yana kwanciya kuma idan hankula sun kwanta ana samun fahimtar juna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164