Sanatocin APC da PDP sun kara bisa furucin da Keyamo ya yi kan Atiku

Sanatocin APC da PDP sun kara bisa furucin da Keyamo ya yi kan Atiku

Rikici kan zaben shugaban kasa na 2019 ya barke a ranar Laraba a kwamitin tantancewa na majalisar dattawa lokacin da sanatocin jam’iyyun All Progressives Congress ( APC) da na Peoples Democratic Party ( PDP) suka samu sabanin ra’ayi kan furucin da kakakin kungiyar kamfen din Buhari, Festus Keyamo ya yi cewa dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar barawo ne.

Matsala ya fara ne lokacin da Keyamo ya gurfana a gaban kwamitin bankuna, inshore da sauran hukumomin kudi na majalisar dattawa domin a tantance shi cikin shugabannin hukumar Nigeria Deposit Insurance Corporation ( NDIC).

Don haka sai zukata suka baci lokacin da shugaban kwamitin, Sanata Rafiu Ibrahim (PDP Kwara ta Kudu), ya tunatar da Keyamo furucin da ya yi kwanan nan cewa Atiku Abubakar barawo ne.

Sanatocin APC da PDP sun kara bisa furucin da Keyamo ya yi kan Atiku
Sanatocin APC da PDP sun kara bisa furucin da Keyamo ya yi kan Atiku
Asali: Depositphotos

Amma sai mambobin APC a kwamitin kamar su Danjuma Goje, Umar Kurfi, Fatimah Raji Rasaki da sauransu suka nuna rashin amincewa da Sanata Ibrahim inda suka gargade shi da kada ya hada siyasa da shirin tantancewa.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon cin hanci: Mawallafin zai gurfana a gaban majalisar dokokin Kano a yau

A wani lamari na daban mun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta yi magana game da karan da aka aikata gaban Kotu na kin binciken wani tsohon Gwamna.

Kwanaki wani Bawan Allah Osadalor Ochie ya shigar da Hukumar EFCC kara a gaban Kotu saboda ta ki gabatar da bincike kan Kwamared Adams Oshiomhole wanda yayi Gwamna a Jihar Edo tsakanin 2008 har zuwa shekarar 2016.

Osadalor Ochie ya matsawa EFCC lamba inda ya nemi Kotun Tarayya ta tursasa ayi bincike game da zargin da ke kan wuyan tsohon Gwamnan. Hakan ta sa dole Kotu ta nemi a soma binciken Oshiomhole wanda ya bar kujerar Gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng