Majalisar dokoki ta kafa kwamiti domin binciken rikicin hukumar NHIS

Majalisar dokoki ta kafa kwamiti domin binciken rikicin hukumar NHIS

Majalisar dokokin kasar ta kafa wata kwamiti domin bincikenrikicinda yaki ci yaki cinyewa tsakanin ma’aikatan hukumar Inshorar Lafita ta kasa da babban sakataren hukumar Usman Yusuf.

Diri Douye mai wakiltar jihar Bayelsa ya ja ragamar muhawarar a majalisar inda ya bayyana cewa abin yayi kamari ta yadda har sai da akai ta kai ruwa rana tsakanin ma’aikatan da babban sakataren hukumar.

Wannan shine karo na biyu da ake dakatar da Yusuf daga aiki kuma duk da haka yaki bin umarnin da kwamitocin dake dakatar dashi take bashi.

Majalisar dokoki ta kafa kwamiti domin binciken rikicin hukumar NHIS
Majalisar dokoki ta kafa kwamiti domin binciken rikicin hukumar NHIS
Asali: UGC

Douye yace saboda wannan dalili ne yake neman majalisar da ta gaggauta daukan mataki kafin hukumar ta zama filin yaki tsakanin shugaban ta da ma’aikatan hukumar.

KU KARANTA KUMA: Kalli hotunan yan shi’a a lokacin da suka shiga fadar shugaban kasa

Shima Tobi Okechukwu mai wakiltan jihar Enugu da yake tofa albarkacin bakin sa ya yi tir da abin dake faruwa a hukumar, haka shima Edward Pwajok dake wakiltan jihar Filato a majalisar ya yi kira ne ga majalisar da tayi ‘taka tsan-tsan wajen daukar matsaya game da abin da yake ta faruwa a ma’aikatar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng