Manyan yan Najeriya 7 da ake bi bashi da adadin kudin da ake bin su
Hukumar da ke kula da kadarorin kasa (AMCON), ta fara tona sunayen wasu manyan ‘yan Najeriya da ke da taurin bashin kuma suka ki zama tare da hukumar domin su warware ko su sauke nauyin da ke kan su.
Jadawalin sunayen mutanen tare da sunayen kamfanonin su, har su 105, An buga jadawalin sunayen mutanen a ranar Litinin, 22 ga watan Oktoba sannan kuma AMCON ta yi barazanar shigo da hukumomin da suka dace a cikin wannan lamarin saboda a tabbatar wadanda aka buga sunayen na su sun biya basussukan da ke kan su.
Ga sunayen wasu daa cikin manyan kasar bakwai da aka amabata:
1. Ifeanyi Ubah, mai Capital Oil and Gas Industries Limited, wanda ake bin kamfanin sa bashin naira biliyan 115
2. Jimoh Ibrahim mai NICON Investment Limited, naira biliyan 59.
3. Wale Babalakin mai kamfanin Bi-Courtney, ana bin kamfanin sa bashin naira biliyan 40.
4. Barth Enaji, tsohon ministan makamashi, wanda ake bin kamfanin sa Geometric Power Industries bashin naira biliyan N29.
5. Tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani ya fito, inda ake bin kamfanin sa mai suna Iorna Global Resources da wasu gungun kamfanoni bashin naira biliyan 42.
KU KARANTA KUMA: Kalli hotunan yan shi’a a lokacin da suka shiga fadar shugaban kasa
6. Kamfanin Buruji Kashamu bashin naira biliyan 13.015.
7. Joshua Dariya, tsohon gwamnan Filato da ke daure zai shafi shekara 14, shi ma ana bin kamfanin sa bashin naira biliyan 6.8.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng