Hamshakan Attajiran Najeriya za su iya fitar da kaf mutanen kasar daga talauci - Economist
Duk da cewa tattalin arzikin Najeriya ne ya fi na kowace kasa karfi da bunkasa a Afrika, Jaridar nan ta Economist tace mutane 3 cikin mutum 5 a Najeriya su na fama ne da masifar talauci na kin karawa.

Asali: Getty Images
Bincike ya nuna cewa manyan masu kudin Kasar nan 5 da ake ji da su za su iya azurta wadanda ke fama da talauci. Dukiyar da wadannan masu kudi su ka mallaka wanda ya kai Dala Biliyan 30 ya isa ya fitar da miliyoyin jama’a daga kangi.
Kudin Alhaji Aliko Dangote wanda ya zarce kowa a kaf Nahiyar Afrika da na Mike Adenuga sai kuma Attajira Foloronsho Alakija, da Pascal Uzoma Dozie da kuma Jimoh Ibrahim za su iya maganin talauci a Najeriya na tsawo shekara guda.
Yanzu dai ana samun rashin daidaituwar dukiya da albarkatun kasa a Najeriya wanda hakan ya sa masu karfi ke cigaba da kara karfi yayin da wadanda talauci yayi wa katutu su ke cigaba da zama cikin fatarar masifa a Kasar na tsawon lokaci.
KU KARANTA: Yadda manyan kamfanoni ke tattara kayan su su bar Najeriya a Gwamnatin Buhari
Munin rashin daidaituwar dukiyar Najeriya dai ya wuce yadda ake tunani a yanzu inda bincike su ka nuna cewa manyan Jihohi irin su Legas, Ribas da Kano sun fi dacewa da karfin kasuwanci yayin da maza kuma su ka fi mata samun dama.
Yanzu haka dai Gwamnatin Kasar ba ta kokari wajen bangaren kiwon lafiya da harkar ilmi. Ba shakka dai Shugaba Buhari ya maida hankali wajen gine-gine da gyara-gyaren hanyoyin titi da dogo wanda hakan zai taimakawa Talakawa.
Haka kuma Gwamnatin Najeriya ta Shugaba Buhari inganta harkar noma domin samun abinci da abin yi a fadin Kasar. Duk da haka dai sai Gwamnatin Tarayya da Jihohi sai sun yi da gaske wajen rufe gibin fataran da ake da shi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng