Zagi da aibanta jami’in Dansandan Najeriya ya jefa wata mata cikin tsaka mai wuya

Zagi da aibanta jami’in Dansandan Najeriya ya jefa wata mata cikin tsaka mai wuya

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Karmo na babban birnin tarayya Abuja ta yanke ma wata ma mai suna Faith Kathy hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni biyu bayan ta ci mutuncin wani Dansanda mai mukamin DCO tare da zaginsa.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito Dansanda mai kara, Ijeoma Ukagha ya bayyana ma Kotun cewa wasu jami’an Yansanda ne suka kama Faith a ranar 18 ga watan Oktoba akan laifin tayar da hankulan jama’a.

KU KARANTA: Masu yi don Allah: Ta sadaukar da filinta don gina Masallaci, ta bada gudunmuwar dubu 800

Toh amma da suka garzaya da iya ofishin Yansanda, sai ta buge da zagin wani babban Dansanda tare da ci masa mutunci a yayin da ya fara gudanar da bincike akan sababin zuwanta ofishin, don haka ya kara da cewa laifin ya saba ma sashi na 155 na kudin hukunta laifi.

Sai dai bayan an karanto mata laifin da ake tuhumarta da shi a gaban Kotun, sai Uwargida Faith ta amsa laifinta, amma ta yi ma kotu magiya akan ayi mata sassauci, saboda bacin rai ya kwasheta ga zagin Dansanda.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkalin Kotun, Inuwa Maiwada ne ya yanke ma Faith hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni biyu, amma yace tunda ta nemi sassauci daga wajen Kotu, ya bata zabin biyan taran kudi Naira dubu uku kacal.

Daga karshe Alkali Maiwada ya gargadi Faith da kada ta kuskura ta kara tafka laifin da zai sa a gurfanar da ita gaban Kotu, sa’annan ya shawarceta da ta zama mace mai kaunar zaman lafiya da makwabtanta.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Nassarawa na cigaba da kokarin ceto wani Dan jarida mai suna Jerry Gana dake aiki da hukumar gidan rediyon Nassarawa, wanda masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da shi a ranar Lahadin data gabata tare da abokinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel