Ernest Shonekan na nan da ran sa bai mutu ba – Gwamnatin Jihar Ogun

Ernest Shonekan na nan da ran sa bai mutu ba – Gwamnatin Jihar Ogun

Mun ji cewa Gwamnatin Jihar Ogun tayi maza ta musanya rade-radin da aka tayi na cewa tsohon Shugaban kasar nan Ernest Shonekan ya rasu. Gwamnatin Jihar tace Shonekan yana nan kalau da ran sa.

Ernest Shonekan na nan da ran sa bai mutu ba – Gwamnatin Jihar Ogun
Gwamnatin Jihar Ogun da Iyalin Ernest Shonekan sun tabbatar yana raye
Asali: UGC

A yammacin jiya Talata ne aka fara yada labarin cewa Ernest Shonekan ya rasu. Sai dai Sakataren Gwamnatin Jihar Ogun Taiwo Adeoluwa ya bayyana cewa babu gaskiya a labarin domin har yanzu Ernest Shonekan yana nan a raye.

Taiwo Adeoluwa yayi magana da manema labarai ne a jiyan inda ya tabbatar da cewa tsohon Shugaban kasar bai cika ba. Haka zalika Iyalin tsohon Shugaban na Najeriya sun tabbatarwa gidan Jaridun kasar waje cewa Shonekan yana raye.

KU KARANTA: Wasu tsinannun barayi sun sace takalman Annabi a wata kasa

Ernest Shonekan wanda rikakken Lauya ne kuma Hamshakin ‘Dan kasuwa ya rike Kasar nan ne a matsayin Shugaban rikon-kwarya bayan mulkin Sojan Janar Ibrahim Babangida na lokaci kadan kafin Janar Sani Abacha yayi juyin mulki.

Cif Shonken wanda yanzu yake rike da sarautar gargajiya a Jihar sa ta Ogun yana da shekaru 82 a Duniya. Yanzu dai ta tabbata tsohon Shugaban na rikon-kwarya yana nan cikin koshin lafiya a gidan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng