Yanzu Yanzu: Kawu ya nuna bakin ciki kan yawan sauya sheka da yan takarar APC suka yi a Kano
Babban mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara akan harkokin majalisar dokokin kasar, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana sauya shekar da wasu fusatattun ýan takarar APC suka yi zuwa wasu jam’iyyu a jihar Kano a matsayin abun bakin ciki.
Kawu wanda ya kasance dan takarar kujerar dan majalisa mai wakiltan Kano ta Kudu a karkashin inuwar APC yace duk da cewar sauya shekar abun bakin ciki ne, ya kasance sakamakon rashin aldalci da shugabannin jam’iyyar suka yiwa ýan takara.
Yace sakamakon wanin rashin bin tsari wajen gudanar da zaben fidda gwani da aka kammala kwannan nan ne ya haddasa wannan lamari mara dadin ji.

Asali: Depositphotos
A wata sanar da ya saki a Abuja, Kawu yayi kira ga shugaban jam’iyyar da ya dauki mataki domin hana sauran fusatattun ýan takara komawa wata jam’iyyar siyasa yayinda zaben 2019 ke gabatowa.
KU KARANTA KUMA: An sassauta dokar hana fita a Kaduna
Idan za ku tuna kimanin yan takarar jam’iyyar 300 ne suka sauya sheka a jihar Kano yayinda wasu da dama suka sauya sheka a sauran yankunan kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e
Asali: Legit.ng