Yanzu Yanzu: Mutane 9 sun mutu a wani hatsarin babban titin Lagas/Ibadan
Akalla mutane tara ne suka mutu a ranar Talata, 23 ga watan Oktoba bayan wani hatsari da ya afku tsakanin manyan motoci biyu wato Mercedes-Benz Marcopolo da wata Iveco a babban titin Lagas/Ibadan dake yankin Aseese.
Kwamandan hukumar hana afkuwar tsari na jihar Ogun, Mista Clement Oladele ya tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ga kamfanin dilancin labaran Najeriya a Abeokuta.
Oladele ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne sanadiyar gudun da direban bas mai lamba SMK 867 XG ya kwaso.
Ya bayyana cewa bas din ya rasa kansa infa ya je kara da wata babbar mota da aka paka mai lamba AAA XP da misalin karfe 5:30 na safe.

Source: UGC
“Hatsarin ya cika da mutane 42; wanda suka hada da maza 34 da mata takwas.
“Maza uku manya da mata biyu sun ji rauni yayinda maza bawai da mata biyu suka mutu,” inji shi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Lagas
Ya bayyana cewa an mika wadanda suka ji rauni zuwa asibiti mafi kusa yayinda aka kai gawawakin wadanda suka mutu asibitin koyarwa na jami’ar Olabisi Onabanjo, Sagamu, jihsr Ogun.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng