Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Lagas

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Lagas

- Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Lagas da safiyar yau Talata

- Zai halarci taron kaddamar da iyakar ECOWAS a Seme

- Buhari zai hade da takwaransa na jumhuriyar Benin a wajen taron

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Lagas domin taron kaddamar da iyakar ECOWAS a Seme.

Shugaban kasar wanda ya isa jihar a safiyar ranar Talata, 23 ga watan Oktoba zai halarci karramar da rundunar sojin Najeriya, sojin ruwa da sojin sama suka shirya masa kafin ya dangana ga Seme Border.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Lagas
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Lagas
Asali: Depositphotos

Shugaban kasar da takwaransa na jumhuriyar Benin, Patrice Talon za su gabatar da mika sabon iyakar ta kasashen Afrika (ECOWAS) a Seme-Krake da Neope-Akanu a Badagry.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Boko haram sun kai hari wani kauye kusa da Chibok sun kashe mutane 2

An tsaurara matakan tsaro a yankunan jihar daban-daban, wanda suka hada da jami’an yan sanda, sojin sama, kwastam, hukumar shige da fice da kuma yan sandan farin kaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng