Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Edo ta rantsar da sabon mataimakin kakakinta

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Edo ta rantsar da sabon mataimakin kakakinta

Majalisar dokokin jihar Edo ta rantsar da Mista Justin Okonoboh a matsayin sabon mataimakin kakakinta.

Okonoboh ya kasance mamba mai wakiltan mazabar Igueben a majalisar dokokin jihar.

Ya yi rantsiwar kama aiki da misalin karfe 10:06 na safiyar ranar Talata, 23 ga watan Oktoba.

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Edo ta rantsar da sabon mataimakin kakakinta
Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Edo ta rantsar da sabon mataimakin kakakinta
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa an tsige Edoro ne bayan wani korafi da dan majalisa mai akiltan Oredo ta gabas, Hon Osaigboyo Oyoha ya gabatar, kan zargin almubazaranci da kudi da kuma yin ayyukan da suka saba ma jam’iyya da cin hanci da rashawa akan mataimakin kakakin majalisan.

Tsigewar nashi ya yayi sanadiyar hafar da rudani yayinda shi da wasu magoyabayansa suka yi kokarIn nuna turjia.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Boko haram sun kai hari wani kauye kusa da Chibok sun kashe mutane 2

Da abubuwa suka daidaita, an dakatar da mataimakin kakakin majalisar, mamba mai wakiltan mazabar Owan ta gabas Folly Ogedengbe, da wani mamba mai wakiltan Etsako West, Gani Audu, na tsawon watanni uku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng