Rashin samun Haihuwa ya sanya na kwanta da 'Diya ta - Igbaniba
Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, wani Matashin Mahaifi mai shekaru 35 a duniya, Michael Igbaniba, ya shiga hannu jami'an tsaro na 'yan sanda a sanadiyar kwanciya da diyar cikin sa har na tsawon shekaru biyu.
Michael yayin amsa laifin sa ya bayyana cewa ya tsinci kansa cikin wannan mummunar aika-aika ne a sanadiyyar rashin samun haihuwa da iyalin sa da idanun sa suka rufe wajen neman yalwar 'ya'ya.
A yayin da tura ta kai bango dangane da wannan mummunan lamari ya sanya wannan Budurwa mai shekaru 15 a duniya ta yi korafin Mahaifin ta ga ofishin hukumar 'yan sanda na Iso Koko dake unguwar Agege a jihar Legas.

Asali: Facebook
Da ta ke zayyana korafin ta a karshen makon da ya gabata, wannan Budurwa ta bayyana cewa ta yi shayin furta wannan lamari sakamakon barazanar Mahaifin ta na daina biya ma ta kudin Makaranta a sanadiyar soyayyar ta ga Karatu.
KARANTA KUMA: Rayuka 23 sun salwanta, 17 sun jikkata a rikicin jihar Kaduna - SEMA
Mista Igbaniba yayin titsiyen jami'an 'yan sanda ya tabbatar da cewa shawarwari na abokai da 'yan uwa suka sanya ya afka cikin wannan lamari da a cewar su zai samu biyan bukata cikin gaggawa.
Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, CSP Chike Oti, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari inda ya bayyana cewa tuni bincike na diddigi ya kan kama domin gurfanar da Igbaniba a gaban Kuliya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng