'Yan sanda zasu gurfanar da dan tsurku a kan bayar da bayanan karya a kan shugaban NIA

'Yan sanda zasu gurfanar da dan tsurku a kan bayar da bayanan karya a kan shugaban NIA

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta gurfanar da wani mutum, Dakta Kassim Abdulganiyu, saboda ba su bayanan karya da ya jawo su ka je bincike gidan tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Ambasada Ibrahim Zakari.

Shi dai Dakta Abdulganiyu, mazaunin gida mai lamba 21 dake Colorado Crescent a Abuja, ya sanar da jami'an 'yan sanda cewar Ambasada Zakari ya boye makamai a gidansa ba bisa ka'ida ba, amma bayan jami'an 'yan sandan sun birkice gidan Ambasada Zakari basu samu komai ba.

Dakta Abdulganiyu ya sanar da hukumar 'yan sandan ne a watan Agusta, 2018, cewar an jibge wasu mugayen makamai a gidan Ambasada Zakari da ke kan titin Sultan a unguwar Malali da ke garin Kaduna.

'Yan sanda zasu gurfanar da dan tsurku a kan bayar da bayanan karya a kan shugaban NIA
'Yan sanda zasu gurfanar da dan tsurku a kan bayar da bayanan karya a kan shugaban NIA
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: El-Rufai ya ziyarci wuraren da rikicin Kasuwar Magani ya shafa (Hotuna)

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, ya bayyana cewar basu samu wani kayan laifi ba bayan jami'an 'yan sanda sun caje gidan, ranar 28 ga watan Agusta.

"Mun gudanar da caje a gidan ba tare da maigidan ko wani dan uwansa na wurin ba bayan masu gadin da ke gidan.

"Jami'an 'yan sanda basu san ma cewar gidan na tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Ambasada Zakari, ba ne har su ka nemi takardar neman izinin caje gidan," a cewar Moshood.

Ko a kwanakin baya ciki watan Satumba an samu kwatankwacin irin wannan matsalar bayar da bayanan karya da su ka kai jami'an 'yan sanda yin dirar mikiya a gidan tsohon minista kuma dattijon kasa, Cif Edwin Clark.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng