Duk lokacin da nayi kokarin sallaman wani mai laifi, shugabannin addini su ka nemi hana ni - Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce a duk lokacin da zai sallami wani jami’in gwamnati da aka kama da laifin sata, sai shugabannin addini da na siyasa da dama su nemi da kada yayi hakan.
Da yake magana a taron kwamitin tattalin arzikin Najeriya kan rashawa da doka a Abuja a ranar Litinin, 22 ga watan Oktoba, mataimakin shugaban kasar yace shugabannin Najeriya kan toshe hanya a duk lokacin da za’a yaki cin hanci da rashawa.
Naire Woods, gidauniyar Blavatnik School of Government a jami’ar Oxford, wadanda suka jagoranci taron sun bukaci Osinbajo da ya fada ma taron wanda ke kiran shi a lokacin da yayi yunkurin sallaman mai laifi.

Asali: Depositphotos
A nashi martanin Osinbajo yace: “Zan so nayi Magana kan shugabannin Najeriya, kuma bai dace mutun ya kasance mai fadada zance ba, abode mutanen da ked a hanyar ganinka kai tsaye na iya kasancewa shugabannin siyasa, shugabannin addini, manyan yan kasuwa, duk ma wanda ked a alaka da kai.
“Akwai wani tsari inda mutane za su iya ganin, ‘mai zai hana ka kyale wane na dan lokaci?’wanda hakan wata matsala ne na daban. Ba kira daya ba, kira da dama.”
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fusatattun ma’aikata sun tsare dakataccen sakataren NHIS a ofishinsa (hotuna)
Mataimakin shugaban kasar yace gwamnati na aiki sosai don ganin ta magance lamarin cin hanci da rashawa inda ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya zama mataimakin shugaban kasa, ya bayar da gudunmawa sosai wajen magance cin hanci da rashawa kuma abun ya zarce tunanin sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng