Takardun bogi: Razak Atunwa bai yi bautar kasa na NSYC ba

Takardun bogi: Razak Atunwa bai yi bautar kasa na NSYC ba

Wani bincike da Jaridar Premium Times ta gudanar ya fallasa cewa ‘Dan takarar PDP na zaben Gwamna a Jihar Kwara watau Hon. Razak Atunwa bai yi bautar kasa bayan ya kamalla karatun Jami’a ba.

Takardun bogi: Razak Atunwa bai yi bautar kasa na NSYC ba
'Dan takarar Gwamna da Saraki ya tsaida bai da takardun shaidar NYSC
Asali: UGC

Yanzu haka dai an gane cewa Razak Atunwa yana amfani ne da takardun shaidar hidimar kasa na NYSC na bogi. Dokar kasa dai tace dole sai mutum yayi wa Kasa hidima sannan zai iya rike wani babban ofis wanda hakan ya sa wata Minista ta ajiye aiki.

Rasak Atunwa dai bai yi aikin NYSC ba duk da ya gama Digiri a wata Jami’ar Landan yana da shekaru 23 da haihuwa. Sai a 2005 ne Atunwa ya dawo Najeriya inda ya rike mukami a Gwamnatin Kwara karkashin tsohon Gwamnan Jihar Bukola Saraki.

‘Dan takarar yana ikirarin cewa yayi bautar kasa tsakanin 1995 zuwa shekarar 1996, sai dai ta tabbata hakan ba gaskiya bane. Yanzu dai ana iya daure sa na shekaru 14 idan ta tabbata bai da gaskiya a Kotu kamar yadda dokar kasar Najeriya ta tanada.

KU KARANTA: Abubuwan da jama’a ke fada a dalilin sauya-shekan Sanata Shehu Sani

A takardar shaidar na Razak Atunwa za a ga sa hannun Birgediya Janar Walter Oki. Sai dai a wancan lokaci watau 1996, Janar Oki bai zama Shugaban NYSC ba. Sai a 2002 ne aka nada Janar Walter Oki ya jagoranci Hukumar bautar kasar na NYSC.

Ana zargin cewa Razak Atunwa ya rika amfani da takardun bogi ne lokacin da ya zama Kwamishina a 2005 har zuwa lokacin da ya zama Kakakin Majalisar dokoki a 2015 kafin ya tafi Majalisar Wakilan Tarayya inda yake wakiltar Kwara a 2015.

Ba dai yau aka fara bankado masu amfani da takardun karya a Gwamnatin Najeriya ba. Daga cikin Ministocin Buhari akwai da-dama wadanda ba su yi NYSC ba. Sai dai binciken ya nuna cewa na wannan ‘Dan takarar Gwamnan ya fi fito fili a zahiri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng