Zargin sata: An taso tsohon Gwamnan Edo Adams Oshimhole a gaba

Zargin sata: An taso tsohon Gwamnan Edo Adams Oshimhole a gaba

Kwanakin baya ne wani babban Fasto mai kare hakkin Bayin Allah marasa karfi kuma babban ‘Dan gwagwarmaya a Kudancin Najeriya watau Osadolor Ochie ya shigar da Adams Oshimhole Kotu.

Zargin sata: An taso tsohon Gwamnan Edo Adams Oshimhole a gaba
Ana zargin Oshiomhole ya saci kudin jama’a a lokacin yana mulki
Asali: Depositphotos

Osadolor Anthony Ochie ya maka Shugaban na Jam’iyyar APC mai mulki da kuma Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ne a wani babban Kotun Tarayya da ke zama a Birnin Tarayya Abuja kwanaki.

Rikakken ‘Dan gwagwarmayan ya shiga da EFCC Kotu ne a dalilin watsi da binciken da aka nemi tayi a kan tsohon Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomhole. An shigar da korafin zargin satar da ke kan Gwamnan amma EFCC tayi gum.

KU KARANTA: Fitaccen Sanatan APC ya koka da kashe-kashen da ake yi a kasar nan

Bishof Osadolor Ochie yace yana da hujjoji da ke nuna irin mahaukaciyar satar da Adams Oshiomhole yayi a lokacin yana Gwamna don haka yake neman a bincike sa. Ganin EFCC tayi kunnen kashi ne ya shiga Kotu da kan sa.

Ochie wanda Malamin addini ne, ya kai karar tsohon Gwamnan na APC ne ta hannun wani Lauya Dr. Ehiogie West Idahosa wanda yanzu an kuma fara yi masu yadda su ke so. Ochie dai ya bayyana cewa ba ya tare da wata Jam’iyyar siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng