Dalibai 7, 942 zasu samu tallafin kudin karatu na N694, 682, 000 daga gwamnatin jahar Kaduna
Hukumar kula da kudin tallafi na jahar Kaduna, ta sanar da ware makudan kudi naira miliyan dari shida dan casa’in da hudu, da dari shidda da tamanin da biyu (N694, 600, 000) don biyan daliban jahar kudin tallafi na shekarar 2017/2018.
Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban hukumar, Hajiya Jummai Dikko ce ta sanar da haka a ranar Juma’a 19 ga watan Oktoba a garin Kaduna, inda tace hukumar zata fara biyan kudin da zarar kwamishinan ilimi ya samu amincewa daga majalisar zartarwa ta jahar.
KU KARANTA: Wani babban Sarki a Najeriya ya bayyana ma Duniya sabuwar Amaryarsa
Majiyar LEGIT.com ta ruwaito Jummai na cewa; “Kudin tallafin da ake baiwa dalibai ya zama wani ginshi ga da dama daga cikin daliban dake manyan makarantun gaba da sakandari, dalibai kan biya kudin makaranta, kudin daki da kuma ciyar da kansu da kudin.

Asali: UGC
“Gwamnatin nan ta sauya tsarin bada kudin tallafi ta hanyar da zai amfani dalibai da yawa musamman duba da halin rayuwa da ake ciki a yanzu, don haka sabon tsarin zai kara ma dalibai kwarin gwiwa dangane da karatun da suke yi.
“Dalibai dubu goma sha biyar da dari bakwai da ashirin da biyu ne suka nemi gurbin samun tallafi, amma an zabi dalibai dubu bakwai da dari tara da arba’in da biyu daga kananan hukumomin 23 na jahar Kaduna da suka cancan samun tallafin na shekarar 2017/2018, da haka ne gwamnan jahar Kaduna ya bamu umarnin mu fara biyan kudin.” Inji ta.
Idan za’a tuna a ranar 10 ga watan Oktoba ne daliban jahar Kaduna suka baiwa gwamnatin jahar wa’adin kwanaki 21 da ta biyasu kudaden tallafinsu na shekaru uku da bata biya ba, amma bayan kwana biyu sai shugaban daliban jahar Kaduna, Yahaya Abdullahi ya basu tabbacin za’a fara biyansu kudin cikn yan kwanaki.
Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng