Bidiyon cin hanci: Majalisar dokokin jihar Kano ta aika sammaci ga editan Daily Nigerian
Kwamitin da majalisar dokokin jihar Kano ta kafa domin binciken ingancin bidiyon da ke nuna Gwamna Abdullahi Ganduje na karban rashawa ya aika sammaci ga babban editan Daily Nigerian, Malam Ja’afar Ja’afar da ya gurfana a gaban ta.
Jaridar Daly Nigerian c eta wallafa bidiyon wanda ya haifar da kace-nace.
Sakataren kwamitin, Nujtafa Aminu ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Kano a ranar Juma’a, 19 ga watan Oktoba.

Asali: Depositphotos
Aminu ya ce kwamitin a wasika mai kwanan wata 19 ga Oktoba ta bukaci Ja’afar day a gurfana a gabanta a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba a zangon majalisar.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta bukaci EFCC da ta binciki badakallar hukumar aikin Hajji
Ya ce an samar da ingantaccen tsaro don bad an jaridan kariya yayinda ake sanya ran zai amsa wasu tambayoyi kan bidiyon day a saki a yanar gizo.
A cewarsa, kwamitin ta rigada ta ziyarci kwamishinan yan sandan jihar, Mista Rabi’u Yusuf da daraktan yan sandan DSS domin neman goyon bayansu da tsaro.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng