Sasanta Atiku da Obasanjo: Kungiyar Musulunci ta kare Gumi da Kukah, tayi na’am da hada addini da siyasa

Sasanta Atiku da Obasanjo: Kungiyar Musulunci ta kare Gumi da Kukah, tayi na’am da hada addini da siyasa

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi watsi da tunanin mutane na cewa mutane su bar siyasa saboda addini, cewa mutanen da suka yi watsi da siyasa saboda cewar su Musulmai ko Kirista ne daga karshe sukan kasance a karkashin mutane da basu da tsron Allah.

A cewar kungiyar kare hakkin Musulmin, kamata yayi addini da siyasa su tafi a tare domin akan samu kauce hanya da sauransu a inda aka bar mulki a hannun mutanen da basu tsoron Allah.

MURIC ta bayyana hakan ne bayan mutane na ta cece kuce akan sansanta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakinsa Alhaji Atiku Abubakar.

Sasanta Atiku da Obasanjo: Kungiyar Musulunci ta kare Gumi da Kukah, tayi na’am da hada addini da siyasa
Sasanta Atiku da Obasanjo: Kungiyar Musulunci ta kare Gumi da Kukah, tayi na’am da hada addini da siyasa
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Atiku Abubakar: Zan tabbata na yiwa Buhari ritaya a siyasa don ya koma Daura a 2019

A wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola yace babu wani aibu a abunda ya wakana a Abeokuta, jihar Ogun.

Ya bukaci mutane da su daina sukar babban malamin nan na Musulunci da ke zaune a Kaduna, Shekh Ahmed Gumi da babban fasto din cocin Catholic Diocese of Sokoto, Reverend Matthew Kukah, cewa suna da yancin halartan duk wani taro da zai hada kan mutanen Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng