An kama wata mahaukaciya da ke bara dauke da N200,000 a Anambra
A ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba an kama wata mahaukaciya da ke bara dauke da kudi kimanin N200,000 a jihar Anambra.
An tattaro cewa jami’an gwamnatin jihar kimanin wata guda da ya gabata sun kafa wata hanyar kore irin wadannan mutanen ta ofishin kwamishinan harkokin mata da ci gaban jama’a.
An rahoto cewa ana yawan ganin matar wacce ke cikin shekaru na 50 a mararabar Aroma, a Awka babbar birnin jihar.
Jami’an gwamnatin suyi kokarin kama ta ne domin su kai ta gidan mahaukata a jihar.

Asali: Getty Images
Wata majiya na gwamnati da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa jami’an sun tunkari matar ne sannan suka yi mata jagora zuwa motarsu, amma ta turje cewar ba zata bar kayanta ba.
“Don haka sai jami’an suka fada mata cewar ba za su kwashi tarkacen da ta kira da dukiyanta ba, amma ta dauki duk wani abu mai muhimmanci a gar eta. A lokacin ne ta zazzage buhun sannan ta fito da kudin.
“Abun ya bamu mamaki domin bata da hankali kuma tana yawan bara a mararabar Aroma da ke Awka.
A hakan sai aka sami N200,000 a hannunta.” Inji majiyar.
KU KARANTA KUMA: Magu bai ce babu abunda zai faru idan Fayose ya mutu a tsare ba - EFCC
Wani mai wucewa da ya kira sunansa da Tony ya kara da cewa “Na san wannan matar a kullun ta kan kasance cikin tsafta duk da yanayinta. Tana siyam abinci duk lokacin da ta ji yunwa.
“Bata bayyana tushen kudinta ba, amma yana iya kasancewa daga wanda take samu a wurin baranta.
“Haka kuma an dade ana zargin cewa maza na zarya wurinta a cikin dare sannan su hadu.”
Duk kokari da aka yi domin jin ta bakin minisatar harkokin mata, Misis Ndidi Mezue bai samu ba domin taki daukar waya balle amsa sakon waya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng