Magu bai ce babu abunda zai faru idan Fayose ya mutu a tsare ba - EFCC
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) tace mukaddashin shugaban ta, Mista Ibrahim Magu bai taba fadin cewa babu abunda zai faru idan har tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya mutu a tsare a hannun hukumar ba.
Hukumar EFCC ta bayyana hakan a wata sanarwa daga kakakinta, Mista Wilson Uwujaren a ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba.
Hukumar yaki da rashawan tace akwai wani faifai murya na bogi dake yawo a shafukan zumunta wanda aka jiyo wai Magu na fadin cewa babu abunda zai faru idan Fayose ya mutu a hannun su.

Asali: Twitter
Duk yunkurin da hukumar EFCC din tayi don mallakar faifan a ranar Alhamis bai cimma nasara ba amma sun bukaci jama’a da su share zancen.
EFCC tace tsohon sakataren labarai na jam’iyyar ne ke ta yada faifan.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose na fada ma jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) duk abunda ya sani game da naira biliyan N4.685 da ake zargin an cire daga ofishin tsohon mai ba kasa shawara akan harkar tsaro.
KU KARANTA KUMA: Gwamnoni za su sanya dokar ta baci kan harkar ilimi a jihohin su
Fayose ya yi Magana a jiya bayan ya kwashe tsawon sa’o’i 72 a tsare.
Ya amince da sanin batun kudi naira biliyan 1.299 da tsohon karamin ministan tsaro, Mista Musiliu Obanikoro ya kai masa a cikin jirgi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng