2019: Takarar Atiku Abubakar tana kara karfi a Najeriya
Bloomberg tayi wani rubutu kwanan nan inda tayi bayanin cewa ‘Dan takaran Shugaban kasa a Jam’iyyar adawa a Najeriya Atiku Abubakar yana iya mamayar Jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2019.

Asali: Twitter
Atiku Abubakar mai shekaru 71 wanda zai kara da Shugaba Muhammadu Buhari na iya yin irin abin da APC tayi wa PDP a lokacin Goodluck Jonathan. Yanzu dai Atiku yana kokarin jawo hankalin Mala’u da manyan kasar.
Kafin yanzu dai ana tunanin cewa APC za tayi wa PDP dukan babban bargo ne a 2019, sai dai da alama lissafi ya fara canzawa a Kasar domn kuwa ana ganin Atiku zai tabuka wani abu inji wani Masanin tattali Bismarck Rewane.
KU KARANTA: An yi wa baitul malin Najeriya kar-kaf cikin kwanaki 13
Haka-zalika wata matsala ita ce kusoshin Gwamnati irin su Shugabannin Majalisa Bukola Saraki, da Yakubu Dogara da manyan Gwamnoni na Yankin Arewa irin Aminu Tambuwal ba su tare da Shugaban kasa Buhari a yanzu.
Yanzu haka dai Atiku yana ta kokarin shawo kan wasu manya da ke bangaren Yarbawa da Yankin Neja-Delta da kuma Yankin Arewacin Najeriya. Ana tunani ma Atiku ka iya samun gudumuwa wajen manyan Malaman addini a kasar.
Wani abu kuma shi ne tsofaffin Sojojin kasar ba su tare da Shugaba Buhari a yanzu. Sannan kuma Atiku ya zabi yayi takara da Inyamuri wanda zai taimake sa a Kudancin kasar. Sai dai hakan na nufin sai yadda Yarbawa su kayi a zaben.
Asali: Legit.ng