Dalilai 5 da ya sa Turawa suka damu da Saudiyya
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar mumunan matakin ladabtarwa a kan Saudiyya, idan har ta tabbata cewa ita ked a hakkin kashe shahararren dan jaridar nan Jamal Khashoggi.
Saudiyyar ta sha alwashin mayar da kakkausan martani ga duk wani mataki mai tsauri da kasashen Yammacin duniya za su dauka a kanta.

Asali: UGC
Abubuwan da akan ka iya haifarwa:
1. Samar da mai da farashinsa
Saudiyya ce ke da kusan kaso 18 cikin dari na arzikin mai da aka tabbatar a duniya, kuma ita ce kasa ta daya da ta fi sayar wa kasashen duniya man, kamar yadda kungiyar kasashe masu arzikin mai ta duniya (Opec) ta bayyana.
Wannan ya sa Saudiyya na da matukar muhimmanci a kasashen duniya.
Saboda haka uzura mata zai iya haifar da durkushewar tattalin arzikin duniya.
2. Kwantiragin soji
A shekara ta 2017 Saudi Arabia ce ta uku a girman kasafin tsaro a duniya, kamar yadda bayanan cibiyar bincike kan zaman lafiya ta duniya, suka bayyana.
A wannan shekara kasar ta kulla yarjejeniyar sayen makamakai ta dala biliyan 110 da Amurka, da wata karin dama ta kara yarjejeniyar ta kai har ta dala biliyan 350 a tsawon shekara 10.
Wan nan yarjejeniya ita ce mafi girma a tarihi don haka ake ganin gwamnatin Saudiyya za ta iya mayar da martani a kan duk wani takunkumi da kasashen Ymma za su iya sanya mata, ta yadda za ta karkata ga China da Rasha wajen neman biyan bukatun dakarunta.
KU KARANTA KUMA: Uba ya kai karar dansa mai damfara ta intanet ga hukumar EFCC (hoto)
3. Tsaro da ta'addanci
Kasashen Yammacin duniya sun jaddada cewa Saudi Arabia tana taka gagarumar rawar gani wurin tabbatuwar tsaro a Gabas ta Tsakiya, tare da kawar da tsattsauran ra'ayi da ta'addanci.
Kasar wadda ita ce cibiyar Musulunci, mamba ce a cikin kasashen da suka yi taron-dangin da Amurka ke jagoranta wajen yaki da kungiyar IS.
4. Hadin kai a yankin
Saudiyya ta yi aiki sosai tare da Amurka domin hana Iran tasiri a yankin na Gabas ta Tsakiya.
Kasashen Musulmin masu bin akidar 'yan Sunni da kuma 'yan Shia suna rikici da juna a fakaice a fadin yankin na Gabas ta Tsakiya tsawon shekara da shekaru.
A sharhin labaransa, Aldakhil ya yi gargadin cewa kyautatuwar dangantaka tsakanin Saudi Arabia da Rasha a sanadiyyar takunkumin Amurka, da kuma kulla wata sabuwar yarjejeniyar makamai da Moscow, ka iya kaiwa ga kusanci da Iran har ma ya iya kaiwa ga sasantawa da ita.
5. Kasuwanci da zuba jari
An kuma bayyana cewa sanya takunkumin akan Saudiyya zai iya sanadiyar hana kamfanonin Amurka shiga kasuwar Saudiyya.
Asali: Legit.ng