Salihu Sagir Takai bai da niyyar barin Jam’iyyar PDP zuwa APC
Labari ya zo mana a jiya cewa daya daga cikin manyan ‘Yan takarar Gwamna a Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar PDP Malam Salihu Sagir Takai bai da niyyar barin Jam’iyyar ya koma APC mai mulki.

Asali: UGC
A baya mun ji kishin-kishin din cewa Salihu Sagir Takai na daf da tserewa daga Jam’iyyar ta PDP bayan da Hukumar zabe na kasa na INEC ta ba Surukin Sanata Rabiu Kwankwaso watau Abba Kabir Yusuf takardar shaidar takara.
Duk da dai wannan mataki da Hukuma ta dauka bai yi wa Malam Salihu Takai dadi ba, ‘Dan siyasan bai da shirin shiga Jam’iyyar APC mai mulki a Kano. Tun 2011 dai Takai yake neman kujerar Gwamnan Kano amma bai samu sa'a ba.
Kawo yanzu dai Takai da Jama’an sa ba su tunanin ficewa daga PDP duk da abin da ya faru. Shugaban masu taya Takai yakin neman zaben Gwamna a kafofin zamani watau Muhammad Bashir Aminu yayi mana wannan karin haske.
KU KARANTA: An tabbatar da Bindow a matsayin 'Dan takarar Gwamna a Adamawa
Akwai dai masu neman babban ‘Dan siyasar wanda yayi takarar Gwamna sau 2 a Jihar Kano ya fice daga PDP zuwa wata karamar Jam’iyya domin yayi takaran sa a 2019. Sai dai babu lissafin komawa Jam’iyyar APC mai rike da mulki a Jihar.
An dai yi tunani cewa Salihu Takai ne zai yi takara a PDP sai kuma Sanata Rabiu Kwankwaso da Mabiyan sa su ka sauya sheka. Wannan ya sa tun lokacin ake kukan ‘Yan Kwankwasiyya sun karbe PDP har wasu manyan PDP su ka koma APC.
Yanzu dai haka Jam'iyyar PDP tana kokarin sasanta kan manyan 'Ya 'yan na ta domin kar ta yi asara a 2019 kuma akwai yiwuwar a ba Salihu Takai takarar Mataimakin Gwamnan Kano a Jam'iyyar a 2019.
Asali: Legit.ng